Siyasar Saudiyya: Watakil Sarki Salman ya sauke dansa daga Yarima mai jiran gado, kan kisan Khashoggi
- Ana zargin yarima Mohammed bin Salman da mutuwar wani dan jarida
- A farko kasar ta Saudi bata yi wani abu akan batansa ba
- Bincike ya nuna cewa an shirya yin kisan ne

Asali: Depositphotos
Ana zargin yarima Mohammed bin Salman akan rasuwar wani dan jarida wanda aka rasa shi bayan ya shiga ofishin jakadancin kasar Saudia dake Istanbul.
A farko Saudi Arabia batayi wata hobbasa ba akan batan nashi kafin a zarge su da dawowa da gawar shi a 2 ga watan October.
DUBA WANNAN: An kashe sarkin Adara a Kaduna
A ranar Alhamis babban dan Khashoggi mai suna Jamal Khashoggi ya hada kan iyalanshi suka bar Saudia zuwa Washington DC.
Hukumar bincike ta Saudi tace da alama wannan kisan an shirya shi ne sannan sunaci gaba da gudanar da binciken don gano wanda keda hannu a ciki.
Yanzu kuma rahotannin cikin gida na cewa bayan yawan korafe-korafe daga malamai da masu fada a ji, boye ko a fili, Sarki Salman na duba yiwuwar sauke dan nasa daga matsayin mai jiran gado, musamman bayan alamu sun nuna ya san da kisan da aka yi wa Jamal.
Wannan na nufin akwai yiwuwar a dauko kanensa Khalid, ko kuma wani daga cikin tsofin 'ya'yan Sarakunan, musamman daga gidan Fahad ko Faisal ko ma Abdalla.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng