Yanzu-yanzu: Jam'iyyu siyasa 79 ne sun mika sunayen 'yan takarar shugabancin kasa - INEC
- INEC ta bayyana cewar jam'iyyu 79 ne suka gabatar mata da sunayen 'yan takarar shugaban kasa
- Hukumar ta kuma bayyana cewar jam'iyyu 89 sun gabatar da sunayen 'yan takarar sanata 1,803
- Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu ya ce hukumar za ta fitar da cikaken bayani kan dukkan 'yan takarar da aka mika sunayensu

Asali: Depositphotos
A halin yanzu da ake tunkarar babban zaben kasa na 2019, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa jam'iyyun siyasa 79 ne suka mika sunayen 'yan takarar shugabancin kasarsu.
Wannan sanarwan da fito ne daga bakin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu a wata jawabi da ya yiwa da manema labarai a hedkwatan hukumar da ke Maitama a Abuja.
DUBA WANNAN: Tashin hankali: 'Yan fashi sun sace bindigu masu yawa daga ma'ajiyar makaman 'yan sanda
Shugaban ya ce baya ga sunayen 'yan takarar shugaban kasa 79 da aka gabatarwa wa hukumar, jam'iyyu 89 kuma sun gabatar da sunayen yan takara 1,803 domin takarar kujerar sanata da kuma sunyen 'yan takara 4,548 domin takarar mazabu 350 na tarayya.
Farfesa Yakubu ya yi alkawarin cewar hukumar za ta bayyana sunayen dukkan 'yan takarar da jam'iyyunsu nan ba da dadewa ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng