Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin ficewa daga jam’iyyar

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin ficewa daga jam’iyyar

Tsohon kwamishina a gwamnatin jahar Kano ta Malam Ibrahim Shekarau, kuma tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Salihu Sagir Takai ya bayyana dalilin da yasa ya sake sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano.

Takai ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da rediyo BBC Hausa, inda yace rashin adalcin jam’iyyar PDP yasa shi ficewa daga cikinta, kuma ya koma PRP, a cewarsa rashin adalci da son kai ne yayi ma jam’iyar PDP katutu a Kano.

KU KARANTA: Wani Musulmi ya kusa mutuwa a sanadiyyar rikicin Kaduna amma Kirista ya cece shi

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin ficewa daga jam’iyyar
Takai
Asali: Depositphotos

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito a kwanakin baya ne dai aka samu rahotanni dake nuna PDP ta tsayar da Takai a matsayin dan takararta na gwamnan jahar Kano a zaben 2019, duk da cewa jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani kuma surukin Kwankwaso, Yusuf Abba ne ya lashe. Amma kuma PDP ta tabbatar da takarar Abba daga bisani.

Yadda abin ya faru shine, an gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a gidan jagoran jam’iyyar a jahar Kano Sanata Rabiu Kwankwaso, sai dai yan takarar gwamna a jam’iyyar basu shiga zaben ba face Abba Yusuf, da wani guda daya.

Bayan kamala zaben aka sanar da Abba a matsayin wanda ya lashe zaben, sai dai sauran yan takarar sun yi korafi game da wannan zabe, inda suka bayyana shi a matsayin dauki daura, don haka suka garzaya ga uwar jam’iyyar ta kasa.

Bayan sauraron korafe korafensu ne sai uwar jam’iyyar ta tattaro shuwagabannin jam’iyyar ta Kano, inda suka zauna suka tabbatar da Takai a matsayi sabon dan takarar gwamnan jahar Kano a PDP. Suma daga nan tsagin jam’iyyar dake karkashin Kwankwaso suka kalubalanci matakin da PDP ta dauka.

Wannan cece kuce ne dai ya sanya uwar jam’iyyar yin karatun ta natsu, inda ta sake daukan wani sabon matakin daya tabbatar da Abba Yusuf surukin Kwankwaso a matsayin halastaccen dan takararta a zaben gwamnan jahar Kano na 2019

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng