Sanata Shehu Sani ya fadi su waye makiyan Najeriya na zahiri

Sanata Shehu Sani ya fadi su waye makiyan Najeriya na zahiri

- Sanata Shehu Sani, sabon mamba a jam'iyyar PRP bayan fitar sa daga APC, ya yi Alla-wadai da kisan mutane da sunan addini

- Sanata Sani, ya bayyana masu fakewa da addini domin rura wutar rikici a matsayin makiyan Najeriya na zahiri

- Sanata Sani na wadannan kalamai ne ta shafinsa na Tuwita a jiya, Laraba, 24 ga watan Oktoba, 2018

Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana masu fakewa da addini domin rura wutar rikici a matsayin makiyan Najeriya na zahiri.

Sanata Sani, sabon mamba a jam'iyyar PRP bayan fitar sa daga APC, ya yi Alla-wadai da kisan mutane da sunan addini.

Dan majalisar ya bukaci mabiya addinai da su yi watsi da duk wani kira da ba na zaman lafiya ba.

Sanata Sani na wadannan kalamai ne ta shafinsa na Tuwita a jiya, Laraba, 24 ga watan Oktoba.

Sanata Shehu Sani ya fadi su waye makiyan Najeriya na zahiri
Sanata Shehu Sani
Asali: Twitter

"Dole ne mu yi Alla-wadai da kisan mutane da sunan addini. Ma su aikata kisa da sunan addini su ne manyan makiyan Najeriya kuma dole ne mu hade kai domin mu yake su," a cewar Sanata Sani.

A ani labarin Legit.ng mai alaka da wannan, kun ji cewar hukumar 'yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane 22 da ta ke zargin na da alaka ta kai tsaye da kisan mutane a kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai yau, a Abuja.

DUBA WANNAN: Babban abin da ya girgiza ni a matsayina na mataimakin shugaban kasa - Osinbajo

"Mun kama mutane 22 da ke da alaka ta kai tsaye da kisan jama'a, su na ajiye wurin mu kuma su na taimakawa jami'anmu da muhimman bayanai a kan rikicin," a cewar Moshood.

Moshood ya kara da cewar yanzu haka zaman lafiya ya dawo tare da bayyana cewar an sako wasu manyan mutane da aka sace yayin rikicin.

Kazalika ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin wadanda su ka rasa 'yan uwansu sanadiyar rikicin.

"Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya yi Alla-wadai da afkuwar rikicin. Sannan ya kafa wani kwamitin bincike na musamman da zai gudanar da bincike a kan kisan jama'ar da ba su aikata laifin komai ba," kamar yadda Moshood ya fada.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng