Kabilanci: Kaduna ta zama kasasshiyar jiha karkashin El-Rufain APC - Hunkuyi
- Anyi kashe-kashe tsakanin kabilun jihar Kaduna
- An dade ana qiyayya ga juna, kuma babu alamun sassautawa
- Sanata Hunkuyi ya koka

Asali: Depositphotos
Sanatan PDP, mai wakiltar Kaduna ta arewa, ya koka da yawan tashe-tashen hankula da ake samu a Kaduna da kewaye, saboda bambancin kabila, da addini.
A cewarsa, jihar ta ffadi warwas a jarrabawar zaman laffiya, karkashin mulkin APC, da Malam Nasuru Rufai.
Ya kuma yi kira da a fito da basarake da yake zaman garkuwa, hannun mutane da har yanzu ba'a san ko su waye ba, basaraken dai Sarkin Kabilar Adara ne.
DUBA WANNAN: Wadanda Saudiyya ta kashe a shekarun nan
An sanya dokar ta baci a jihar, inda aka takaita zirga-zirga da ma baza jami'ai a lunguna da sakoki na jihar.
Babu dai ranar da kasar nan zata zauna lafiya, tunda kabilunta sun kasa zama lafiya da juna, manya da qanana, kowa ya tsani kowa, na bangaren kabila daban, na bangaren addini daban.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng