Kafin zabe, makamai 7,000 hukumomi suka kama suka lalata a kasar nan
- An samu nasarar lalata makamai 7,000 da basu da lasisi
- Muna fama da karuwar makamai da ake shigowa dasu Nageriya
- Duk wani mai farin kaya daya mallaki wani makami ya sani ya sanya rayuwar sa cikin hatsari

Asali: Twitter
Wani kwamiti d aka kafa ya samu nasarar lalata makamai sama da 7,000 wadanda basu da lasisi a Nageriya.
Jagoran kwamitin yace sun kama makamai 640 a jahar Benue,sannan sun samu sama da 625 a jahar Katsina yayin da suka kama 5,970 a Zamfara.
Gaba daya adadin makaman da muka tattara yakai 7000 Jagoran ya bayyana haka ne a wajen wani taro a Abuja ranar Litinin.
Ya kara da cewa Nageriya tana cikin fargabar yawaitar shigowa da makamai a akeyi zuwa cikin kasar.
DUBA WANNAN: Siysar Yanki: Abubuwan da Kwankwaso zai iya koya daga Tinubu
Yace mafi yawan makaman da ake samu ana samunsu ne a hannun fararan hula, duk wanda ya mallaki wani makami ba bisa ka'ida ba to fa ya sanya rayuwar sa cikin hatsari.
Zamuci gaba da bawa Nageriya koyan baya wajen kawo karshen mallakar makami ba tare da izini ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng