2019: Sanata Bala ya zabi Baba Tela a matsayin mataimakinsa

2019: Sanata Bala ya zabi Baba Tela a matsayin mataimakinsa

Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja kuma dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a babban zaben 2019 a Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya zabi Baba Tela a matsayin mataimakinsa.

Sanarwan ta fito ne daga bakin Sakataren yada labarai na jam'iyyar Yayanuwa Zainabari yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Bauchi.

2019: Sanata Bala ya zabi Baba Tela a matsayin mataimakinsa
2019: Sanata Bala ya zabi Baba Tela a matsayin mataimakinsa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wata mace ta yi karar mijinta a kotu bisa gazawarsa wajen biya mata hakin kwanciyar aure

Ya ce shugabanin jam'iyyar, da dan takarar gwamnan da kuma masu ruwa da tsaki a jam'iyyar sun zabi Tela ne saboda biyaya da sadaukar da kai da yayi domin ganin jam'iyyar PDP ta cigaba a jihar.

Zainabari ya ce da farko Sanatan ya yi niyyar fitowa takarar Sanata ne a yankin Bauchi ta Arewa a zaben na 2019 amma daga baya aka roki shi ya janyewa Sanata mai ci yanzu, Suleiman Nazif wanda ya koma jam'iyyar daga PDP.

"Da farko ya yi niyyar takarar sanata ne a mazabar Bauchi ta Arewa amma ya janye wa Sanatocin da suka shigo jam'iyyar daga APC. Hakan ya sa aka zabe shi a matsayin mataimakin dan takarar gwamna a jam'iyyar mu," inji shi.

Ya yi kira ga mambobin jam'iyyar su mara musu baya kuma su zabi 'yan takarar jam'iyyar idan zabe ya zo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164