Sunaye: Hukumar Sojin Sama ta yiwa manyan jami'ai 27 canjin wurin aiki
Hukumar Sojin Saman Najeriya ta yiwa wasu manyan jami'anta 29 canjin wuraren ayyuka kamar yadda ta saba yi daga lokaci zuwa lokaci domin kara inganta aiki.
Sanarwar da ta fito daga kakakin hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola ta ce sabbin AOCs din da aka yiwa canji sun hada da Air Vice Marshal Mohammed Suleiman wanda aka ajiye shi a Kaduna sannan AVM Idi Amin wanda aka mayar da shi jihar Enugu.
Ya ce, an nada AVM Dayo Adeluoye a matsayin Direktan Tsare-tsare na Hukumar Tsaro (DHQ), AVM Olusoji Awomodu shi kuma yanzu shine Direktan Gwaje-Gwaje kana AVM Tunde Awoyoola shi kuma Direktan Ayyuka na DHQ.

Asali: Facebook
DUBA WANNAN: El-Rufai ya ziyarci wuraren da rikicin Kasuwar Magani ya shafa (Hotuna)
Shi kuma AVM Ismaila Kaita an nada shi a matsayin mataimakin shugaban Makarantar Horas da Hafsoshin Soji (NDA), AVM Mohammed Idris shi kuma an nada shi mataimakin shugaban cibiyar binciken sararin samaniya yayin da AVM Charles Ohwo yanzu shine Direktan Ayyuka na hedkwatar NAF.
Har ila yau, Air Commodore Christopher Egwoba yanzu shine Direktan Gwaje-Gwaje a hedkwatan NAF, Air Commodore Amos Bulus kuma Direktan Kimiyar Sadarwa duk dai hedkwatan NAF yayinda Group Captain Francis Edosa shine kwamandan 307 Executive Airlift Group da ke Abuja.
Sauran sun hada da Group Captain Abiodun Oyekunle a matsayin shugaban riko na kamfanin gine-gine na NAF; Group Captain Haliru Badamasi a matsayin Direktan ayyuka na NAF sai Wing Commander Dooyum Laha a matsayin kwamandan makarantar koyan tukin jirgin sama na 41 da ke Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng