Rikicin Kaduna: El-Rufa'i ya zagaya sassan da rikici ya shafa, ya ziyarci asibitoci (Hotuna)
- Da sanyin safiyar yau, Ltinin, ne gwamnan jihar Kaduba, Malam Nasir El-Rufa'i, ya gudanar da wani zagayen rangadin sassan da jaririn rikicin da ya barke jiya a garin Kaduna ya shafa
- Kazalika, gwamnan ya ziyarci asibitin St. Gerards da na Barau Dikko domin jajantawa wadanda rikicin ya shafa kuma ke samun kulawa a asibiti
- A daren jiya, Lahadi, ne shugaba Buhari ya yi alla-wadai da rikicin na jihar Kaduna, da ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane 55
Da sanyin safiyar yau, Ltinin, ne gwamnan jihar Kaduba, Malam Nasir El-Rufa'i, ya gudanar da wani zagayen rangadin sassan da jaririn rikicin da ya barke jiya a garin Kaduna ya shafa. Daga cikin unguwannin da El-Rufa'i ya ziyarta, domin jajantawa jama'a tare da ba su tabbacin cewar gwamnati ta shawo kan lamarin, akwai Kabbala da Bakin Ruwa.
Kazalika, gwamnan ya ziyarci asibitin St. Gerards da na Barau Dikko domin jajantawa wadanda rikicin ya shafa kuma ke samun kulawa a asibiti.
A jiya, Lahadi, ne gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sanarwar saka dokar ta baci tare da hana mutane fita na tsawon sa'o'i 24 a kwaryar birnin Kaduna da kewaye domin dakile yaduwar jaririyar tarzomar da ta tashi a garin.

Asali: Depositphotos

Asali: Twitter
A wata sanarwa da Samuel Aruwan, mai taimaka gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna a bangaren yada labarai, ya fitar, ya bayyana cewar dokar hana fitar za ta fara aiki nan take. Dokar ta bacin na zuwa ne kwanaki uku bayan barkewar rikici mai nasaba da addini a kasuwar Magani da ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane 55 da asarar dukiya mai tarin yawa.
DUBA WANNAN: Hawa Yinusa, matar da ke jagorantar fashi da satar mutane ta shiga hannu
Kazalika, a daren na jiya ne shugaba Buhari ya yi alla-wadai da rikicin na jihar Kaduna, da ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane 55, tare da bayyana cewar ba zai taba yarda da wofantar da ran bil'adama da zubar da jini ba. Buhari ya ce babu wani addini da ya yarda da tashin hankali.
Shugaba Buhai ya bayyan cewar ya bawa rundunar 'yan sanda damar daukan dukkan matakin da zai kai ga dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Kaduna. Kazalika ya bayyana cewar ya umarci shugaban rundunar 'yan sanda ya tura runduna ta musamman tare da sanar da shi halin da ake ciki a kan lokaci.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng