Babban magana: APC ta zargi Gwamna Tambuwal da daukan nauyin yan sara suka

Babban magana: APC ta zargi Gwamna Tambuwal da daukan nauyin yan sara suka

Jam’iyyar APC reshen jahar Sakkwato ta mayar da martani ga gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal bisa zarginta da yayi na cewa wai za ta yi amfani da yan sara suka wajen yakin neman zabe a shekarar 2019, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar LEGIT.com ta ruwaito kaakakin jam’iyyar, Sambo Bello Danchadi ne ya mayar da martanin, inda yace Gwamna Tambuwal tare da jam’iyyarsa ta PDP ne ke daukan nauyin yan sara suka a jahar, tare da aikace aikacen da suka yi.

KU KARANTA: Duk inda Obasanjo ya bi damu, ya zama wajibi mu bi shi sau da kafa – Gumi

Jam’iyyar ta bayyana kisan da aka yi ma wani matashi mai shekaru 23 a yayin bikin karrama gwamnan, a matsayin hujjarta da ta kafa dake nuna gwamnan ne ke daure ma yan sara suka gindi a jahar.

Bugu da kari, jam’iyyar ta zargi gwamnan da barazanar sallamar ma’aikatan gwamnatin jahar, musamman masu goyon bayan jam’iyyar ta APC, daga karshe kuma tace bata da yan daba domin ita jam’iyya ce mai kaunar zaman lafiya.

Tsatstsamar dangantaka ta shiga tsakanin Gwamna Tambuwal da jam’iyyar APC ne tun bayan ficewarsa daga APC, inda ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP, har ma ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar ta PDP.

A game da goyon bayan da jigon jam’iyyar ta PDP, kuma gwamnan jahar Ribas, Nyesom Wike ya baiwaTambuwal a yayin zaben fidda gwani na PDP kuwa, Wiken yace baya da na sani, duk kuwa da cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben da kuri’a fie da dubu daya, yayin da Tambuwa ya samu kuria dari shida da yan kai.

Sai dai shima tsohon uban gidan Tambuwal a siyasar jahar Sakkwato, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako ya bayyana cewa ficewa daga APC da Tambuwal yayi ba karamin kuskure ya tafka ba, amma ba zai gane ba har sai sun fayyace masa haka a zaben 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng