Bayan kasar Habasha, Rwanda ma tace zata baiwa mata kujeru 50 a kowanne mataki na gwamnati
- Kasar Rwanda na gabashin Afirka kamar Habasha
- Ana ware mata a sha'anin mulki, inda wasu addinai da al'adu ke ma ganin kamar su ababen mallaka ne
- A yanzu mata na samun ilimin Boko kuma an daidaita gado tsakaninsu da maza
Kwana biyu kawai da aka sami labarin cewa kasar Ethiopia, watau Habasha, mai kyawawan mata, ta ayyana kujerun gwamnati da na majalisu cewa rabi dole a baiwa na mata, suma gwamnatin Rwanda mai kabilu daban daban, sun dauki wannan mataki.
Shugaban Kasar, Paul Kagame, ya dade yana suya wa kasar taza fasali, inda bayan kisan qare dangi da aka yi a 1994, yanzu kasar ta zamo gaba-gaba a Afirka, a kyau da tsari.
A kwanakin baya ma, ya rufe masallatai da coci, inda yace duk sun hana jama'a bacci, kuma basu koyar da sana'a sai cinye ma talakawa kudi da sunan kaisu ga tsira.
DUBA WANNAN: An kamo masu kokarin kashe shugaban kasa
A kasashe da dama dai, mata kan zama saniyar ware ne, inda wasu al'adu da addinan ma, kan ce matan basu kai maza ba, kuma gado da shaida ma, baza'a basu daidai da maza ba.
A wannan zamani dai, mata sun yunkuro, sun fito takara, sun kuma goga da maza, sun kuma gwada yin mulki, abu da wasu ke ganin bai kamace su ba, sun kuma yi karatun boko, sun sami jari sunyi kasuwanci duk dai a kasashe masu taso wa.
Kasashen Turai, tuni suka wuce wannan shinge, suka bar na baya sai dai su kamo qafa.
A Najeriya, kasashen da dama, ciki har da Najeriya, mata basu da wata katabus, musamman a gwamnati da siyasa, sai yadda maza suka yi dasu, don bassu da jari, basu kuma da gata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng