Za'a samar da qarin Megawatt 4,200 a lantarkin Najeriya kwanan nan
- Gwamnatin tarayya tana shirin kara samar da wutar lantarki
- Za'a samu karin megawatt 4200 a watanni 12 zuwa 18 masu zuwa
- Aikin samar da wutar zai tabbatar da samuwa da kuma rarrabata

Asali: UGC
Ministan Masana'antu, cinikayya da hannun jari, Dr. Okechukwu Enelamah, a jiya ya bayyana shirin Gwamnatin tarayya na kara samar da wutar lantarki ga Masana'antu da guraren da suke bukatar wutar a kasar.
Kamar yanda ya fada,NIPCAC ce ke shirya hakan karkashin shugabancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, gurin samar da Megawatts 4200 na wutar lantarki a cikin wata 12 zuwa 18.
Jimillar aiyukan samar da wutar lantarki 8 kenan.
DUBA WANNAN: Buhari: Zamu gama da Boko Haram
A bayanin da yayi wa manema labarai, Enelamah, wanda shine mataimakin shugaban kungiyar, yace yanzu haka aikin Alaoji yayi nisa gurin samar da wutar lantarki ga yankin kudu maso gabas da suka hada da Onitsha, Aba, Nnewi da Ihiala.
Yace aikin samar da wutar na hadin guiwa ne tsakanin Gwamnatin da yan kasuwa inda ake samar da wutar tare da rarrabata ga mabukata.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng