Jihar Kaduna ta samu lambar yabo wajen harkar kasuwanci
Wasu Jihohi na kokari matuka na ganin an rage sarkakiya wajen harkar kasuwanci a Najeriya. Babban bankin Duniya tace daga cikin Jihohin da su kayi namijin kokari bana akwai irin su Jihar Kaduna.

Asali: UGC
Wani babban Jami’in babban Bankin Duniya, Olufunke Olufon, ya fitar da wani rahoto a Abuja wanda ya bayyana cewa Jihohi irin su Kaduna, Enugu, Abia, Lagos da Anambra sun yi zarra a bana wajen bangaren habaka kasuwanci.
Jihar Kaduna ce ta zo ta farko a wannan rahoto na bankin Duniya inda ta samu maki 65.97. Kaduna ce kan gaba wajen saukin yin rajista da kuma dabbaka ayyuka sannan kuma ta zo ta 5 a kaf fadin Najeriya wajen saukin yin kasuwanci.
KU KARANTA: Rikicin kabilanci ya sabbaba kisan mutane da asarar gidaje a Kaduna
Jihohi 29 ne dai su ka kawo tsare-tsare iri-iri da za su taimaka wajen ganin an cire sarkakiyan da ake samu wajen yi wa kamfani rajista da sauran su. Jihar dai ita kadai ce ta ciri wannan tuta daga kaf sauran Jihohin Arewacin Kasar.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yabawa Mataimakin sa Arc Barnabas Y Bala Bentex wanda yake jagorancin kwamitin da aka kafa domin wannan aiki. Ana sa rai dai abubuwa su fi haka kyau a Kasar a shekarar badi.
Kun san cewa a jiya ne Gwamna Nasir El-Rufai da Gwamna Simon Lalong na Filato su ka gana da ‘Yan wasan kwaikwayon a fadar Shugaban kasa inda ‘Yan fim din su kace za su ba APC gudumuwa a 2019.
Asali: Legit.ng