Zaben fidda gwani: APC da Shehu Sani sun yi ma gwamnan jahar Kaduna ba zata
Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta tabbatar da Sanata Shehu Sani a matsayin halastaccen dan takara daya tilo da ta amince ma ya sake tsayawa takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a zaben 2019, duk da cewa bai fafata a zaben fidda gwani ba.
Majiyar Legit.com ta ruwaito wata kwamitin sauraron korafe korafe da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole ya kafa ce ta wanke Shehu Sani daga dukkanin tuhume tuhumen da jam’iyyar APC reshen jahar Kaduna take yi masa.
KU KARANTA: Wata sabuwa: An fallasa wani gwamnan jam’iyyar PDP dake amfani da shaidar haihwua ta bogi
Rahoton da kwamitin mai dauke da mutane biyar ta fitar ne ya tabbatar da wannan matsaya na jam’iyyar, kwamitin a karkashin jagorancin Ferfesa Oserheimen Osunbor ta wanke Sanatan soso da sabulu, inda tace Shehu Sani kai dan takarar da ta sani a Kaduna ta tsakiya.

Asali: Depositphotos
Wannan mataki da APC ta dauka bai yi ma APC ta jahar Kaduna dadi ba, sakamakon tsatstsamar dangantaka dake tsakaninta da Sanatan, wanda rikicin ya samo asali ne tun lokacin da aka yi hannun riga tsakanin gwamnan da Sanatan.
Wannan rikicin ne ya y sanadiyyar gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai da jam’iyyar APC ta Kaduna suka dauki gabaran goyon bayan hadimin gwamnan, Uba Sani don ya kwace kujerar Sanatan da Shehu Sani yayi dare dare akai.
Ganin cewa baya shiri da APC ta Kaduna, hakan ne ya sa Sanata Shehu Sani yaki amincewa da zaben fidda yan takarkaru da ta shirya wanda Uba Sani ya lashe, inda shi kuma ya ruga ga uwar jam’iyyar APC ta kasa wanda ta bashi tabbacin za ta bashi takara shi kadai.
A yanzu dai a iya cewa kurungus kan kusu game da rikicin takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya, sai dai wani hanzari ba gudu ba, masana siyasar Kaduna na ganin jam’iyyar APC ta Kaduna ba zata hakura ba, za ta iya garzayawa kotu akan wannan batu.
Ku biyo mu a https://www.legit.com
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng