Ta auri kanta da kanta bayan da ta ga mijin mai iso ba

Ta auri kanta da kanta bayan da ta ga mijin mai iso ba

- Lulu Jemimah mai shekaru 32 ta auri kanta

- Dalibar jami'ar Oxford din tayi haka ne don gajiya da tayi akan zancen aure

- Amaryar da ta auri kantan tayi wa yan bikin bayanin rashin angon

Ta auri kanta da kanta bayan da ta ga mijin mai iso ba
Ta auri kanta da kanta bayan da ta ga mijin mai iso ba
Asali: Depositphotos

Lulu Jemimah mai shekaru 32, daliba a jami'ar Oxford, yar asalin kasar Uganda ta auri kanta a gaban yan biki 30 da suka kasance shaidu.

Dalibar jami'ar Oxford din ta gaji da matsawar da yan uwanta suka mata akan maganar aure. A don haka ne ta yanke hukuncin auren kanta inda ta gayyaci kawaye da abokan arziki domin su shaida.

Lulu dai tace aure shine abu na karshe a ranta. Ta kashe £2 na kudin tasi zuwa gurin bikin auren, inda sauran abubuwan kawaye suka bata kyauta domin shirya bikin.

Amaryar da ta auri kantan ta yiwa yan bikin bayanin rashin angon. Inda ta sanar dasu cewa iyayen ta sun damu da hukuncin ta amma tace hakan ne yafi dacewa gareta da kuma karatun ta.

DUBA WANNAN: Labarai da duminsu a tasharmu ta Legit Hausa

Dalibar jami'ar Oxford din mai digiri na biyu a fannin rubutun fasaha daga kasaitacciyar jami'ar, tace ; 'Ina da buri a rayuwata kuma inason cika buri na na zama mai karantarwa. Amma yan uwana sun takura ni da tambayar yaushe zanyi aure, yaushe zan fara tara yara.

Babana har jawabin aure na ya rubuta lokacin da na cika shekara 16. Kowacce ranar zagayowar haihuwa ta sai mahaifiyata tayi min addu'a samun miji nagari. Amma gaskiya ni babu wannan a raina. Babu hakan a gaban. "

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng