Jakadan Ingla: Dokar hana barayi tserewa ta Buhari na kan daidai

Jakadan Ingla: Dokar hana barayi tserewa ta Buhari na kan daidai

- Wasu lauyoyi guda biyu sunyi suka akan hukuncin da shugaban kasa ya zartar

- Gwamnatin ta bawa AGF damar karbe duk wani abu da suke tantama akansa

- Yana da matukar muhimmanci ga Nageria ta kawo karshen cin hanci da rashawa

Jakadan Ingla: Dokar hana barayi tserewa ta Buhari na kan daidai
Jakadan Ingla: Dokar hana barayi tserewa ta Buhari na kan daidai
Asali: UGC

Babban kwamishinan British a Nageria Mr Paul Akwright yace yanada matukar muhimman ci ga Nageria ta kawar da cin hanci da rashawa a fadin kasar.

A ranar 5 ga watan Yulin ne shugaba Buhari ya sanya wata doka wadda ta bawa AGF damar karbe duk wani abu da hukumar su bata aminta dashi Ba.

Wasu lauyoyi guda biyu sunyi suka akan wannan doka da aka kaddamar.

DUBA WANNAN: Wani uba ya jibgi wasu malaman makaranta 2 saboda sun yiwa diyar sa bulala

A ranar Alhamis ne kotu tayi watsi da batun nasu inda ta bayyana cewa shugaban yanada ikon sanya duk wata doka da ya so.

A ranar Asabar bayan shafe awanni 48 kotu ta goyi bayan wannan doka inda a take aka tsaida wasu fitattu a Nageria su 50 ga barin fita daga kasar.

Za'aci gaba da bibiyar sahun su har sai an tabbatar da babu wani abu tattare dasu tukunna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng