Karyar rage shekaru: Gwamna PDP ya shiga tsaka mai wuya

Karyar rage shekaru: Gwamna PDP ya shiga tsaka mai wuya

- An gano cewar gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya bawa bawa hukumar zabe takardan shedar haihuwa na bogi

- An ruwaito cewar Wike ya yi karun shekarunsa ne a 1999/2000 domin ya samu damar yin takarar Ciyaman na karamar hukumar Obio/Akpor

- Wani lauya mai wanda ya yi ikirarin sunyi karatun Jami'a da gwamna Wike a Jami'ar Jihar Rivers ne ya shigar da karar a kotu

Wani lauya mai suna Achinike William-Wobodo ya yi karar gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a kotu bisa zarginsa ta amfani da shekarun karya a takardan da ya gabatarwa hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC.

A karar da ya shigar, William-Wobodo ya bukaci kotun ta hana Wike takara a babban zaben 2019 da za'a gudanar a jihar ta Rivers.

Karyar rage shekaru: Gwamna PDP ya shiga tsaka mai wuya
Karyar rage shekaru: Gwamna PDP ya shiga tsaka mai wuya
Asali: Depositphotos

Mai shigar da karar ya bayyana cewar Wike ya yi karin shekarunsa a zaben 1999/2000 lokacin da zaiyi takarar Ciyaman na karamar hukumar Obio/Akpor zuwa 35 alhalin a lokacin shekarunsa basu kai 35 ba.

DUBA WANNAN: Karshen duniya: An kama wasu matasa maza da mata 14 suna tika rawa zigidir a jihar Kebbi

Ya ce Wike ya canja shekarar haihuwarsa daga 13 ga watan Disamba na shekarar 1967 zuwa shekarar 1963 domin ya samu damar shiga takarar. Ya kuma bayar da wasu bayyana da ke nuna cewar shedar haihuwar ma ta bogi ce.

Wanda ya shigar da karar ya yi ikirarin cewar ya san gwamna Wike tun shekarar 1991 a lokacin da suka karatu lauya a jami'ar Jihar Rivers na Kimiyya da Fasaha (RSUST) inda ya ce a wannan lokacin gwamnan ya sha bayyana cewar an haife shi ne a 13/12/1967.

Sahara Reporters ta ruwaito cewar gwamnan da hadimansa suna iya kokarinsu domin ganin an kashe shari'ar kuma wani majiya da ke kusa da gwamnan ya bayyana cewar gwamnan ya yi mamakin yadda abokinsa ya yi masa irin wannan abin gab da zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel