2019: Kungiyar Dariqa ta bayyana dan takarar shugaban kasa da za ta zaba

2019: Kungiyar Dariqa ta bayyana dan takarar shugaban kasa da za ta zaba

- Kungiyar matasa 'yan Dariqa na Najeriya ta bayyana cewar Atiku Abubakar ne za ta zaba a zabeb 2019

- Kungiyar ta yanke shawarar hakan ne saboda irin alkawurran da Atiku ya yi na cewar zai tafi tare da matasa a mulkinsa

- Kungiyar ta ce shugaba Muhammadu Buhari bai cika alkawarin da ya dauka wa matasa ba tun hawarsa mulki a 2015

Ciyaman din Kungiyar hadin kan matasa 'yan Dariqa ta Dariqa Youth Unity of Nigeria DYUN), Sheikh Bashir Jaafar Katsina ya bayyana cewar kungiyar za ta marawa Atiku Abubakar baya a zaben 201 saboda a karkashin mulkinsa ne rayuwar matasa zai inganta.

A hirar da ya yi da Daily Trust a birnin Katsina, Sheikh Jaafar ya ce kungiyar ta yi taro a Jigawa inda ya tattauna kan 'yan takarar shugabancin kasa kuma ta yanke shawarar goyon bayan Atiku saboda alkawurran da ya yi na tafiya tare da matasa.

2019: Kungiyar Dariqa ta fadi dan takarar shugaban kasa da za ta zaba
2019: Kungiyar Dariqa ta fadi dan takarar shugaban kasa da za ta zaba
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Soji sun ragargaji 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Kaduna

Ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi alkawarin cewar za ta dama da matasa amma tun daga shekarar 2015 har zuwa yanzu ba bu wani abinda ta tabukka wa matasan.

"Ina ganin kamar ya da ce mu yiwa Atiku adalci mu goyi bayansa domin ganin ko zai cika alkawurran da ya dauka idan ya lashe zaben," inji Sheikh Jaafar.

A wata rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewar kungiyar karnukan mota na Najeriya sun bayyana cewar suna tare da shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 domin ta gamsu da irin kamun ludayinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel