2019: Manyan Kasar Ibo sun nuna tsagoron adawar su ga Peter Obi

2019: Manyan Kasar Ibo sun nuna tsagoron adawar su ga Peter Obi

Mun samu labari cewa wasu manyan Kasar Inyamurai ba su amince da zabin da Atiku Abubakar yayi na ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa ba a karkashin Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa inda su kace sam ba a tuntube su ba.

2019: Manyan Kasar Ibo sun nuna tsagoron adawar su ga Peter Obi

Ana neman Atiku ya canza Peter Obi idan yana neman nasara a 2019
Source: Facebook

Labari ya zo gare mu cewa Osita Chidoka da wasu Jiga-jigai a Kasar Inyamurai ba su yi na’am da da Peter Obi a matsayin ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa ba inda su ke ganin wasu ne dabam su ka cancanta ba shi ba.

Majiyar mu ta bayyana mana cewa Gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi da kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ne su ka huro wuta cewa sai an canza Obi daga matsayin ‘Dan takaran PDP a 2019.

KU KARANTA: Abin da ya sa ake ganin Ekweremadu zai dace da Mataimakin Shugaban kasa a PDP

Manyan na Kasar Inyamurai sun yi wani zama ne a Jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin kasar su na nuna sam ba su yi amanna da zabin da ‘Dan takarar PDP na Shugaban kasa Atiku Abubakar yayi ba, su na kuma kira a duba lamarin.

Dama dai wasu sun ba Atiku shawara ya dauki Sanata Ike Ekweremadu a matsayin Mataimakin sa sai dai bai yi na’am da hakan ba. Yanzu dai irin su Sanatan da Gwamnonin Yankin ne ke neman juyawa Obi baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel