Babbar Magana: Sojoji sun bazama neman wani janar da ya bata a wata jihar arewa

Babbar Magana: Sojoji sun bazama neman wani janar da ya bata a wata jihar arewa

Tawagar sojojin Najeriya daga sansanin soji na 3 sun bazama neman Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) bayan an neme shi tun ranar 3 ga watan Satumba an rasa.

Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban tawagar masu neman Janar Alkali, ya shaidawa gidan talabijin na Channels a yau, Alhamis, cewar sun tura rundunar soji zuwa yankin Dura Du dake karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.

A cewar Mohammed, bayanai na bayan-bayan nan da suka samu sun tabbatar masu da ganin motar janar Alkali daf da wani tafki a yankin.

Mun zo nan ne bayan samun sahihan bayanai. Mun samu kusan tsawon sati guda muna nan, neman jami’in soja, Manjo Janar M. Alkali (mai ritaya), da har yanzu ba a san inda yake ba,” a cewar Mohammed.

Babbar Magana: Sojoji sun bazama neman wani janar da ya bata a wata jihar arewa
Tafkin da za a yashe a cigaba na neman Janar M. Alkali
Asali: Depositphotos

Mohammed ya kara da cewar hukumar soji zata yi duk mai yiwuwa, koda kuwa ya kama su yashe duk ruwan dake cikin tafkin ne, domin bankado yadda aka yi Janar din ya bace kwanaki kadan bayan ya yi ritaya daga aikin soja.

DUBA WANNAN: Taron dangi: Sojojin Najeriya da na Cameroom sun aika wasu ‘yan Boko Haram lahira, hotuna

Mun zo har inda tafkin rowan yake domin ganin ko zamu samu wani abu da zai kai mu ga gano inda Janar Alkali yake. Wasu bayanai da muka samu sun bayyana cewar an tura wasu motoci cikin tafkin rowan. Rowan yana da zurfi sosai saboda wuri ne da ake hakar ma’adanai. Yanzu haka mun yanke shawarar yashe ruwan tafkin domin samun dammar ganin abinda ke can kasa,” kamar yadda Mohammed ya fada.

Janar Alkali ya bata ne ranar 3 ga watan Satumba bayan ya bar Abuja zuwa Bauchi cikin wata bakar mota kirar Toyoto Corolla. Duk kokarin samun shi ya ci tura saboda wayar sa a kashe take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel