Siyasar Kano: Rikicin mabiya Shekarau da yan Kwankwasiyya ya kai ga Masallacin Juma’a

Siyasar Kano: Rikicin mabiya Shekarau da yan Kwankwasiyya ya kai ga Masallacin Juma’a

A yayin da zabukan shekarar 2019 ke cigaba da karatowa, farfajiyar siyasa na cigaba da kazanta a sanadiyyar banbance banbancen ra’ayi a tsakanin mabiya akidun siyasa daban daban, musamman a jahar Kano.

Wannan hasashe ya tabbata a jahar Kano, inda mabiya siyasar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da aka fi sani da yan Kwankwasiyya da mabiya Malam Ibrahim Shekarau suka yi fito na fito, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

KU KARANTA: Ta fasu: an bayyana makudan biliyoyin da wani Gwamna ya kashe wajen yawo a jirgi

Siyasar Kano: Rikicin mabiya Shekarau da yan Kwankwasiyya ya kai ga Masallacin Juma’a
Amir Kima
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Satumba a yayin daurin aure wani matashi mai suna Ali mai salati a Masallacin Juma’a na Murtala dake birnin Kano.

A yayin wannan fada data kaure tsakanin yan kwankwasiyya da yan Shekarau an jikkata wani matashin Kwankwasiyya guda daya, mai suna Amir Abullahi Kima, tare da tarwatsa taron jama’a da suka halarci daurin auren.

Sai dai wannan sabon tabarbarewar dangantaka tsakanin magoya bayan Kwankwaso da na Shekarau ya samo asali ne tun bayan ficewar Malam Ibrahim Shekarau daga jam’iyyar PDP, inda ya fada APC bayan Rabiu Kwankwaso ya shiga PDP.

A yanzu haka dai a iya cewa siyasar jahar Kano ta sauya zani, musamman ga yadda Shekarau ya yanki tikitin tsayawa takarar Sanatan Kano ta tsakiya, kujerar da Kwankwaso yayi dare dare akai, Alhali a baya Kwankwaso yayi zaton zai hada kai da Shekarau su kada Ganduje.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng