2019: Kwankwaso ya aike da sako mai muhimmanci ga abokan takararsa na PDP

2019: Kwankwaso ya aike da sako mai muhimmanci ga abokan takararsa na PDP

- Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya shawarci sauran 'yan takarar PDP su zama tsintsiya madaurinki daya

- Kwankwaso ya ce hadin kansu a yanzu shine zai tabbatar da cewa za su cigaba da aiki tare bayan anyi zaben fitar da gwani

- Kwankwaso kuma ya yi kira ga shugabanin PDP suyi adalci wajen gudanar da zaben fitar da gwani

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shawarci sauran abokan takararsa a jam'iyyar adawa ta PDP suyi aiki tare da juna saboda kaucewa samun rashin jituwa tsakaninsu bayan babban taron jam'iyyar da za'a gudanar cikin watan Ocktoba.

Kwankwaso, ya yi bayar da wannan shawarar ne a taron da ya yi da 'yan jam'iyyar PDP a yau Laraba a Minna. Ya kuma ce dole dukkan 'yan takarar sun hada kai domin yiwa Najeriya hidima.

2019: Kwankwaso ya aike da sako mai muhimmanci ga abokan takararsa na PDP
2019: Kwankwaso ya aike da sako mai muhimmanci ga abokan takararsa na PDP
Asali: UGC

Ya kuma kallubalanci shugabanin jam'iyyar su yiwa dukkan 'yan takarar adalci wajen gudanar da zaben fitar da gwani domin yin adalci wajen zaben shine zai karfafa jam'iyyar har ta samu nasara a babban zaben da za'yi a watan Fabrairun 2019.

DUBA WANNAN: Babban malamin Islama na son a rage albashin 'yan siyasa

Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya cacaki gwamnatin APC inda ya ce bata tabbuka komai ba kuma har yanzu 'yan Najeriya ba su ga canjin da akayi musu alkawari ba tun a shekarar 2015.

"Canjin da aka kawo a Najeriya kawai shine yunwa, tashe-tashen hankula da rashin ayyukan yi," a cewar Kwankwaso.

Dan takarar kuma ya koka kan yadda titin Suleja zuwa Minna ta lalace duk da cewa titin yana daya daga cikin hanyoyin da jam'iyyar APC tayi alkawarin gyarawa a lokacin yakin neman zabe a 2014.

Ciyaman din PDP a jihar, Tanko Beji, ya tabbatarwa Kwankwaso cewa 'yan PDP reshen jihar Niger za su zabi dan takarar da zai inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel