2019: Wasu manyan ‘yan siyasa a Kano sun yi mubaya’a ga Kwankwasiyya, hotuna

2019: Wasu manyan ‘yan siyasa a Kano sun yi mubaya’a ga Kwankwasiyya, hotuna

A yau, Talata, ne wasu na hannun damar tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, karkashinn jagorancin amininsa, Malam Salihu Sagir Takai, sun yi mubaya'a ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Malam Salihu Sagir Takai, tsohon kwamishina kuma na hannun damar tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce sun yi hannun riga a siyasance da tsohon maigidan nasa.

Takai da Shekarau sun dade tare suna gwagwamarya a siyasa.

Takai na daga cikin kwamishinoni masu fada-a-ji a gwamnatin Kano lokacin da Shekarau ke gwamna.

Shekarau ne ya fara tsayar da Takai takarar gwamana a Kano a shekarar 2011 bayan zangonsa yak are kafin ya kara mara masa baya a shekarar 2015.

2019: Wasu manyan ‘yan siyasa a Kano sun yi mubaya’a ga Kwankwasiyya, hotuna
Kwankwaso da Takai
Asali: Facebook

2019: Wasu manyan ‘yan siyasa a Kano sun yi mubaya’a ga Kwankwasiyya, hotuna
Manyan ‘yan siyasa a Kano sun yi mubaya’a ga Kwankwasiyya
Asali: Facebook

Sai dai a lokacin da ake tunanin cewar Takai zai kasance tare da Shekarau bayan ya canja sheka zuwa APC a ranar Juma’a, sai gas hi Takai ya bayyana cewar zai cigaba da zama a jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau,ya bayyana cewar rashin adalcin da uwar jam’iyyar PDP ta nuna masa ne silar komawarsa jam’iyyar APC.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC ya amince da fitar da biliyan N19.8b don biyan bashin albashin wata 4

Shekarau ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi ga dubban magoya bayansa daga kananan hukumomin Kano 44 a wurin gangamin taron bikin karbarsa a jam’iyyar APC da aka yi a gidansa dake unguwar Mundubawa. A karshe, Malam Ibrahim Shekarau, ya yanki katin shaidar zama dan APC a ofishin jam'iyyar dake mazabar sa ta Giginyu a karamar hukumar Nasara dake Kano a jiya, Lahadi.

Sai dai Malam Takai y ace rashin gamsuwa da dalilan da Shekarau ya bayar ne ya saka shi kin komawa APC tare da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel