Hajjin bana: Dan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan da ya tsinta a Makkah

Hajjin bana: Dan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan da ya tsinta a Makkah

- Wani alhaji daga Najeriya da yanzu haka ke yana gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyyya ya mayar da fiye da N1.4 da ya tsinta a Makkah

- An bayyana sunan alhajin, Musa Mohammed Edotsu, daga jihar Neja kuma ya tsinci kudin ne a sansanin alhazai ‘yan jihar ta Neja a Makkah

- A cewar Isa, daga baya an gano cewsar kudin mallakar shugaban hukumar kula da jin alhazai na jihar Enugu ne, Alhaji Zukalraini Saeed

Wani alhaji daga Najeriya da yanzu haka ke yana gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyyya ya mayar da fiye da N1.4 da ya tsinta a Makkah.

An bayyana sunan alhajin, Musa Mohammed Edotsu, daga jihar Neja kuma ya tsinci kudin ne a sansanin alhazai ‘yan jihar ta Neja a Makkah.

Wani dan jarida daga jihar Neja ,Alhaji Abdul Isa, ya bayyana a hafinsa na dandalin sada zumunta na Whattsapp cewar alhajin ya mayar da kudin da ya tsinta ga wakilan hukumar alhazai ta jihar Neja domin a mayarwa da mai su.

Hajjin bana: Dan Najeriya ya mayar da fiye da miliyan da ya tsinta a Makkah
Alhazan Najeriya

A cewar Isa, daga baya an gano cewsar kudin mallakar shugaban hukumar kula da jin alhazai na jihar Enugu ne, Alhaji Zukalraini Saeed.

DUBA WANNAN: 2019: PDP ta samu karuwa ta wani dan majalisa da ya fita daga APC

Da yake mayar da makudan kudaden gam ai su, shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Neja, Alhaji Abubakar Magaji, ya bayyana cewar sun gano mai kudin ne bayan ganin wasu kayansa cikin kudin da suka hada da fasfo dinsa.

Wanda ya zubar da kudin, Alhaji Zulkalraini, ya bayyana jin dadinsa tare yin godiya ga hukumar alhazai ta jihar Neja bias wannan hali na tsoron Allah da suka nuna. Kazalika ya yi kira ga ragowar alhazai dake aikin hajji da suyi koyi da kyawawan halaye irin na wanda ya dawo da kudin, Alhaji Edotsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel