Sanatan arewa ya gamu da fushin matasan mazabar sa saboda ya koma PDP

Sanatan arewa ya gamu da fushin matasan mazabar sa saboda ya koma PDP

Daruruwan matasa a karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa sun gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewar su da komawar Sanatan su jam'iyyar PDP.

Sanatan yankin, Ubali Shitu, na daga cikin sanatocin da suka canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Matasan sun fara zanga-zangar, duk da ana ruwan sama kamar da bakin kwarya, daga kamfanin sarrafa rake zuwa fadar sarkin Hadejia inda suke rera waken neman Sanatan ya yi murabus daga mukamin sa tare da bayyana cewar "duk wanda ba ya son Buhari barawo ne."

Matasan na dauke da takardu da rubutattun sakonni da suka hada da "bamu yarda da yaran Saraki ba", "duk mai akidar sata ba zai zauna inuwa daya da Buhari ba", "Buhari muke kauna ya zarce har 2023".

Sanatan APC daga arewa ya gamu da fushin matasan mazabar sa saboda ya koma PDP
Matasa yayin zanga-zanga

Akwai rashin jituwa tsakanin Sanata Ubali Shitu da gwamnan jihar Jigawa, Badaru Abubakar. Sanatan ya ci al washin tabbatar da ganin gwamna Badaru bai sake cin zabe ba a 2019.

Shugaban masu zanga-zangar kuma na hannun dama ga gwamna Badaru, Bala Umar, ya shaidawa manema labarai cewar sun yi hakan ne domin tabbatarwa duniya cewar Sanata Ubali ba da yawun jama'ar da yake wakilta ba ya koma PDP.

DUBA WANNAN: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP da dumbin magoya bayansa sun koma APC

"Lokacin da yake jam'iyyar APC zaka samu mutane tare da shi duk lokacin da ya zo Hadejia amma tunda ya koma PDP ba ya iya shigowa Hadejia sai a sace saboda tsoron jama'a," a cewar Umar.

Da aka tuntubi Bala Aji, mai magana da yawun Sanata Ubali, ya bayyana cewar yana da masaniyar zanga-zangar amma ba zai iya cewa komai a kai ba har sai ya tuntubi maigidan nasa.

Sanatan ya gaza samun sukuni a garinsa na Hadejia tun bayan komawar sa jam'iyyar PDP domin ko a yau sai sulalewa ya yi daga garin ya gudu Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel