Dankwambo ya karramaTsohon Gwamnan Jihar Gombe, Marigayi Hashidu

Dankwambo ya karramaTsohon Gwamnan Jihar Gombe, Marigayi Hashidu

Gwamnatin jihar Gombe dake Arewacin kasar nan ta Najeriya, ta sanya wa wani shahararren titi da wata unguwa sunan Marigayi Alhaji Abubakar Hashidu, zababben gwamnan jihar na farko a tarihi da ya riga mu gidan gaskiya a ranar 27 ga watan Yulin wannan shekara ta 2018.

Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Ibrahim Dankwambo, ta sanya wannan suna ne a ranar Juma'ar da ta gabata domin karamma Marigayi Hashidu da cewar ta ya kasance Uba ga kowa a yayin rayuwar sa.

Dankwambo ya bayyana cewa, Marigayi Hashidu yana daya daga cikin mashahuran mutanen da suka taka rawar gani wajen samuwa gami da kafuwar jihar Gombe.

Dankwambo ya karramaTsohon Gwamnan Jihar Gombe, Marigayi Hashidu

Dankwambo ya karramaTsohon Gwamnan Jihar Gombe, Marigayi Hashidu

Yake cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar da ababe da dama cikin jihar domin karrama tsohon gwamnan da a cewar sa har yanzu jihar ba ta kai ga biyan ladan ta ba a gare sa.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin sa ta yi wannan karamci ne domin girmamawa gami da yabawa tsohon gwamnan da ya taka muhimmiyar rawar gani wajen tabbatar da ci gaba a jihar Gombe.

KARANTA KUMA: Mahaifiyar Osama Bin Laden ta yi sharhi bayan shekaru da Mutuwar 'Dan ta

Legit.ng ta fahimci cewa, Marigayi Hashidu ya rike kujerar Ministan ruwa da kuma Ministan noma da raya karkara a lokacin mulkin soji karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Kazalika, masarautar Gombe karkashin jagorancin mai martaba sarkin Dukku, Alhaji Haruna Rashid, ya jinjinawa gwamna Dankwambo dangane da wannan karramci da ya yiwa Marigayi Hashidu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel