Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Rundunar dakarun sojin Najeriya ta Ofireshon lafiya Dole dake aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram 16 tare da kwato wasu motocin yaki da bindigogi.

An yi artabu ne tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da dakarun soji a garin Mairari dake kan hanyar zuwa Monguno ta jihar Borno da misalign karfe 6:50 na ranar juma’a, 27 ga watan Yuli, 2018.

Mayakan Boko Haram sun kai hari a garin na Mairari cikin motoci uku. Saidai nan take dakarun soji suka isa garin bayan samun labarin abinda ke faruwa. Sojojin sun yiwa mayakan rubdugu ta sama da kasa har ta kai ga sun samu nasarar kashe 16 daga cikinsu tare da kama wasu motocinsu na yaki guda biyu.

Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Motar yakin Boko Haram

Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Alburusai da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram

Kazalika dakarun soji sun samu nasarar kwace bindigu da alburusai na mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Yayin artabun, farar hula 4 da soja guda daya sun samu raunuka kuma tuni aka gargazaya das u asibitin sojoji inda a halin yanzu suke samun kulawa.

DUBA WANNAN: An kone daya daga cikin 'yan fashin da suke kashe wata kyakykyawar budurwa

Tuni al’amura sun lafa a karamar hukumar ta Monguno da kewaye, kamar yadda hukumar soji ta sanar tab akin Onyema Chukwu, mataimakin darektan yada labarai na rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole.

Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Motar yakin Boko Haram

Boko Haram: Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu, duba hotuna

Dakarun Soji sun kashe 16 tare da kwato motocin yaki da bindigu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel