Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu Fashi da Makamin Babura a jihar Katsina
A ranar Juma'ar da ta gabata ne hukumar 'yan sanda reshen jihar Katsina, ta bayar da tabbacin ta akan cafke wasu mutane biyu da suka shahara akan fashi da makami musamman na kwace da satar babura.
Kamar yadda hukumar 'yan sandan ta bayyana, wannan mutane biyu a halin yanzu na ci gaba da taimakawa jami'an ta wajen gudanar da binciken yadda suke aiwatar da al'amurran su.
Hukumar ta damuke 'yan ta'addan biyu Muhammad Suleiman da Abdurra'uf Hadi, wanda dukkanin su ba su wuci shekaru 20 a duniya ba kuma mazauna kauyen Tudun Tukare dake karamar hukumar Jibia a jihar.
Kakakin hukumar 'yan sanda, SP Gambo Isah, shine ya bayar da tabbaci kan wannan lamari, inda ya ce hukumar ta samu nasarar cafke Matasan biyu ne yayin da suka yi yunkurin yaudarar wani dan kabubu domin raba shi da abin neman abincin sa.
Matasan biyu sun amsa laifin su tare da fayyace yadda suka makure wani Jamilu Sada, inda suka yi awon gaba da baburin sa da darajar sa ta kai N75, 000, da kuma wayar sa ta salula da darajar ta ta kai N6, 000 a wani kauye Gadare dake iyaka da kauyen Firji na jamhuriyyar Nijar.
KARANTA KUMA: Wasu Mutane 2 sun tsallake Rijiya da baya yayin da Kwantena ta rufta kan Motocin su a jihar Legas
Kazalika 'yan ta'addan sun bayyana yadda suka yiwa wani Sa'adu Idris kwacen baburin sa da darajar sa ta kai kimanin N139, 000 da misalin karfe 9.20 na daren ranar 5 ga watan Yulin da ta gabata.
A yayin haka kuma, hukumar ta samu nasarar dakume wasu mutane hudu da ake zargin su da sace-sacen babura a kauyukan Daulai da Bakiyawa cikin jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng