'Yansandan Kebbi sun rafto masu fashin mota a yankin Yamma mai nisa

'Yansandan Kebbi sun rafto masu fashin mota a yankin Yamma mai nisa

- Barawon motar an taba kama shi kuma an tuhume shi, inda daga baya kotu ta sake shi. Amma bayan satittika kadan aka kara kama shi da laifin satar mota

- A lokacin da wanda ake zargin ke amsa tambayoyi daga manema labarai, yace shi ba satar motar yayi ba, siyan ta yayi Naira 800,000 daga wani

- Kwamishinan yan sandan yace za a cigaba da bincike sannan a tura shi kotu

'Yansandan Kebbi sun rafto masu fashin mota a yankin Yamma mai nisa
'Yansandan Kebbi sun rafto masu fashin mota a yankin Yamma mai nisa

Hukumar yan sandan jihar Kebbi tayi nasarar cafke wani barawon motoci wanda ya Kware a satar motoci a jihar. Yan sanda sunce wanda ake zargin yana zuwa daga Ilorin ne, jihar Kwara satar ababen hawa.

Wanda ake zargin, Peter James, wanda Dan asalin kasar Ghana ne, an kama shi a birnin Kebbi a lokacin da yake kokarin guduwa da wata mota kirar Toyota Camry.

A dubawar da manema labarai sukayi wa wanda ake zargin da kuma sauran masu laifi a shelkwatar yan sandan jihar dake birnin Kebbi, kwamishinan yan sandan jihar, Kabiru Ibrahim yace wanda ake zargin ya dade yana sace motoci yan guduwa dasu inda yake siyar dasu.

DUBA WANNAN: Mutum 10m ne zasu mori kyautar google ta data, ta dindindin

Barawon motar an taba kama shi kuma an tuhume shi, inda daga baya kotu ta sake shi. Amma bayan satittika kadan aka kara kama shi da laifin satar mota.

A lokacin da wanda ake zargin ke amsa tambayoyi daga manema labarai, yace shi ba satar motar yayi ba, siyan ta yayi Naira 800,000 daga wani.

Kwamishinan yan sandan yace za a cigaba da bincike sannan a tura shi kotu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng