Ficewar Kwankwaso daga APC: Matashi ya sha rowan kwatami saboda murna, hotuna

Ficewar Kwankwaso daga APC: Matashi ya sha rowan kwatami saboda murna, hotuna

A yayin da dandalin sada zumunta da kafafen yada labarai ke cigaba da kawo rahotanni da ra’ayoyin jama’a a kan canjib shekar wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC zuwa PDP, jaridar Legit.ngm Hausa ta ci karo da wani labara da shafin wata jarida ya yada dake nuna wani matashi na shan rowan kwatami saboda murnar ficewar Sanatan Kano ta tsakiya daga APC.

A jiya ne sohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, da wasu sanatoci 14 da mambobin majalisar wakilai 37 suka bayyana ficewarsu daga jam’iyyar APC tare da komawa PDP.

Tun a daren jiya jaridar Legit.ng ta kawo makau labrin cewar an samu barkewar murna a birnin Kano bayan samun labarin komawar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso jam’iyyar PDP.

Kwankwaso, Sanatan Kano ta tsakiya, da wasu ragowar Sanatoci 14 sun canja sheka zuwa jam’iyyar PDP, kamar yadda shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya karanta a wasikar da suka ‘yan majalisar suka mika masa.

Ficewar Kwankwaso daga APC: Matashi ya sha rowan kwatami saboda murna, hotuna
Matashi ya sha rowan kwatami saboda murnar ficewar Kwankwaso daga APC

Ficewar Kwankwaso daga APC: Matashi ya sha rowan kwatami saboda murna, hotuna
Matashi ya sha rowan kwatami saboda murna ficewar Kwankwaso daga APC

Masoya Kwankwaso sun fito kwan su da kwarkwata duk da ana tafka rowan sama a garin na Kano, domin nuna farinciki da murnar su bisa barin jam’iyyar APC da Kwankwaso ya yi.

Masoyan na shi sun bayyana cewar sun dade suna jiran irin wannan lokaci domin sun dade da gajiya da irin kallon da ake yi masu a cikin tsarin tafiyar gwamnatin APC a kasa da jiha.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa muka fita daga APC - 'Yan majalisa 37

Saidai kwamishinan raya karkara da birane a jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce suma sun yi murna da ficewar Sanata Kwankwaso domin hakan zai basu dammar yakar shi ka’in da na’in. Kazalika ya bayyana cewar fitar Kwankwaso ba zata shafi kuri’un da shugaba Buhari da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng