Dawo-dawo: An yi bikin jar hula bayan Sanata Kwankwaso ya dawo PDP
Jiya Talata ne tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan ‘Yan Majalisar Kasar su ka tsere daga Jam’iyyar APC su ka dawo asalin Jam’iyyar su ta da watau PDP.
Mun samu labari cewa a wasu wurare a cikin Jihar Kano an yi bikin murna da aka ji cewa Sanatan ya fice daga Jam’iyyar APC mai mulki. Wasu Matasa sun fito sun kona tsintsiyoyi da wuta domin nuna watsi da su kayi da APC.
‘Yan Mata da Samari ne su ka fito cikin jar hula da jan kallabi wanda ke nuna alamar Kwankwasiyya su na kona tsintsiya a jiya da rana. Jam’iyyar APC mai mulki da su Sanata Kwankwaso ya bari ce mai alamar tsintsiya a kasar.
KU KARANTA: Tun ba yau ba Kwankwaso ya bar APC - Kakakin Majalisar Kano
‘Yan Kwankwasiyyan watau Mabiya tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso sun fito su na ihu su na kiran cewa sai Kwankwaso yayi mulkin kasar nan. Mabiya tsohon Gwamnan sun ce Kwankwaso ne zai kora yunwa a Najeriya.
A jiya dai bayan tsohon Gwamnan ya bar APC yayi maza ya gana da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido sannan kuma ya zauna da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu a gidan sa inda har su ka ci abinci.
Ku na da labari cewa Sanatoci fiye da 10 su ka bar APC, daga ciki akwai Sanatocin Bauchi, Jigawa, Adamawa da wasu Sanatoci daga Jihar Kwara. Bayan nan kuma akwai ‘Yan Majalisar Wakilan Tarayya fiye da 30 da su koma PDP.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng