Dalilin da ya sa muka bar APC – ‘Yan majalisa 37 da suka canja sheka
Mambobin majalisar wakilai fiye da 30 da suka canja sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP sun bayyana cewar sun canja sheka ne saboda gazawar gwamnatin tarayya.
Kazalika sun bayyana cewar, rikicin shugabanci da APC ke fama das hi na daga cikin dalilan da ya saka su fita daga jam’iyyar.
‘Yan majalisar sun shiadawa jaridar Vanguard cewar gwamnatin shugaba Buhari na nuna son kai ga wani yanki a rabon mukamai tare da nuna gazawa wajen kulawa da walwala da tsaron mafi yawan mutanen Najeriya.
Daya daga cikin ‘yan majalisar da suka canja sheka, Razaq Atunwa, daga jihar Kwara ya bayyana cewar fitar ta su somin tab ice tare da sanar da cewar wasu da daman a kan hanyarsu ta fita daga APC din.
DUBA WANNAN: Ba zaku bar jam'iyya ku tafi da kujerunku ba - APC zata maka 'yan majalisar da suka fice a kotu
Sannan ya kara da cewar, sun shiga APC ne a 2015 domin hada karfi wuri guda a ceto Najeriya amma daga baya suka fahimci cewar jam’iyyar bata da wata manufa da zata kawo canjin da tayi wa ‘yan Najeriya alkawari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng