Da duminsa: Jerin sunayen ‘yan majalisar wakilai 37 da suka fita daga APC
Wani rahoto da muka samu da dumi dumi yanzun nan ya tabbatar da cewa akalla mambobin majalisar wakilan Najeriya 37 ne suka yi fatali da jam’iyyar APC mai mulki, suka kuma rungumi jam’iyyar PDP, ta adawa.
Daga cikin ‘yan majalisar 37 da suka fice, 33 ne suka koma PDP yayin da wasu 4 daga jihar Osun suka koma sabuwar jam’iyyar ADC ta Obasanjo.
Ga jerin sunayen ‘yan majalisar da suka koma PDP din kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito;
Emmanuel Orker-Jev
Sani Rano
Barry Mpigi
Ali madaki
Dickson Tackighir
Hassan Saleh
Danburam Nuhu
Mark Gbilah
Razak Atunwa
DUBA WANNAN: Da duminsa: Buba Galadima, Shugaban R-APC ya yi hatsari
Ahmed Garba Bichi
Abdulsamad Dasuk
Zakari Mohammed
Canjin shekar ‘yan majalisar ta wakilai na zuwa ne bayan mambobi15 a majalisar dattijai sun canja sheka PDP din, duk a yau.
Komawar ‘yan majalisar ya haifar da hargowa da hayaniya a zauren majalisar ta wakilai, dalilin day a saka ‘yan jam’iyyar APC ficewa daga zauren majalisar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng