2019: Da alamu Shugaba Buhari na kokarin hana Kwankwaso tserewa daga APC

2019: Da alamu Shugaba Buhari na kokarin hana Kwankwaso tserewa daga APC

- An hangi Rabiu Kwankwaso tare da Shugaba Buhari a Aso Villa

- Sanatan ya jagoranci masu neman barin APC zuwa wajen Buhari

- Jam’iyyar APC na kokarin ganin Tsohon Gwamnan bai tsere ba

2019: Da alamu Shugaba Buhari na kokarin hana Kwankwaso tserewa daga APC
Kwankwaso da wasu manyan APC sun gana da Buhari Hoto daga: Abubakar Dadiyata

A jiya da dare ne mu ka samu labari cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a cikin fadar Shugaban kasar na Aso Villa tare da Shugaban APC.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a daren jiya tare da wasu Sanatocin Jam’iyyar APC da su ka fusata da tafiyar a halim yanzu. An yi zaman ne domin dinke barakar da ke Jam’iyyar.

KU KARANTA: An shirya mana makarkashiya domin a hana mu ficewa daga APC – Saraki

Bisa dukkan alamu dai Jam’iyyar APC tana kokarin karshe ne na ganin Sanatan Kano na tsakiya watau Rabiu Kwankwaso bai sauya sheka ba. Gwamnan Jigawa Badaru Muhammadu yana cikin wadanda su ka halarci zaman.

A karshen wancan makon ma dai Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole ya tattaro wasu Gwamnonin Arewa inda su ka gana da Sanata Rabiu Kwankwaso a gidan sa domin hana sa fucewa daga Jam’iyyar APC mai mulki.

Rabiu Kwankwaso ya samu matsala a APC bayan sabani ya barke tsakanin sa da Magajin sa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Ana kishin-kishin din cewa Sanatan da wasu manyan ‘Yan Majalisa za su juyawa APC baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel