Wata mata ta kashe kanta bayan ta gano cewar mijinta ba saurayi bane
Wata ma'aikaciyar jirgin sama, Anissia Batra, da yanke hunkuncin kashe kanta bayan ta gano cewa mijinta, Mayank Singhvi, ya taba auren wata mace daban kafin ya aureta amma bai sanar da ita ba.
A cewar yan sanda, Batra, wacce ke aiki tare da wata kamfanin jirgin sama na kasar Jamus ta shiga cikin bacin rai sosai tun lokacin data gano mijinta ya taba aure a kamar yadda Khaleej Times ta wallafa.
Ta gano cewa Mayank Singhvi ya taba aure ne misalin wata daya da ya wuce. Batra da mijinta sunyi auren soyaya na saurayi da budurwa ne a ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2016.
DUBA WANNAN: Wasu 'yan bindiga sun kashe wani dan acaba haka siddan a Ibadan
"Bai sanar da ita ya taba aure a baya ba. Bayan ta gano cewa yana taba auren, ranta ya baci sosai. Ana zargin cewa sunyi rikici game da batin," inji dan sandan.
An zargin cewa Anissia ta tayi tsalle ne daga benen gidanta a ranar Juma'a. 'Yan uwanta sun zargi cewa Mayank yana dukanta kuma iyayensa suna cin zarafinta saboda kudin sadaki.
An kama Mayank a ranar Litinin kuma an gurfanar dashi gaban kotu a ranar Talata. Kotun kuma ta bayar da umurnin a tsare shi na kwanaki 14.
"Zamu bukaci a bamu shi bayan mun gama tattara bayanai daga bakin shaidu," inji jami'in dan sanda.
Wata kawar Annisia tace yan sanda sun sanar dasu batun gurfanar da Mayank a kotu yayin da ake gab da yin jana'izar marigayiyar.
Hukumar yan sandan tace dan sandan mai shigar da kara ne ya dace ya sanar da iyalan wanda suka shigar da kara game da ranar bayyana a kotun. 'Yan uwan Annisia kuma sun korafi kan yadda yan sandan basu kama iyayen Mayank ba saboda suma suna da hannu cikin mutuwar ta.
Babban jami'in 'yan sanda, Romil Baaniya yace an ware iyayen Mayank daga binciken ne saboda wasu dalilai ba zai iya bayyanawa ba har sai zuwa ranar 20 ga watan Yuli. Yace zasu amsa tambayoyi daga baya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng