IBB da sun yi wata ganawa a sirrance a garin Minna ta jihar Neja
Tsoho shugaban kasa a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da takwaransa na mulkin siyasa, Goodluck Jonathan, sun yi wata ganawar sirri yau, Laraba, a Minna ta jihar Neja.
Tsohon shugaban kasa Jonathan ya isa garin Minna a ayarin wasu manyan motoci guda 6, kamar yadda majiya a gidan IBB ta sanar da jaridar The Nation.
Majiyar ta bayyana cewar daga Babangida da Jonathan sai takarar gwamnan jihar Neja a jam'iyyar PDP, Alhaji Hanafi Muazu Sudan, aka yi ganawar.
Jonathan ya isa gidan IBB dake kan wani tsauni a garin Minna, babban birnin jihar Neja, da misalin karfe 10:00am na safe kuma ya bar gidan da misalin karfe 12:47 na rana.
Kusan dai dukkan tsofin shugabannin Najeriya basa jin dadin mulkin shugaba Buhari, musamman yadda yake bankado badakala da almundahana da gwamnatocin baya suka tafka.
DUBA WANNAN: Abun azimun ne: Buhari ya nemi taimakon kotun duniya ta ICC a yaki da cin hanci
Tuni rahotanni suka bayyana cewar wasu tsofin janar-janar na soji na ganawa domin ganin cewar Buhari bai sake cin zabe a 2019 ba.
Babu rahoton a kan abinda suka tattauna ko dalilin wannan ziyara da Jonathan ya kaiwa IBB.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng