Da duminsa: ‘Yan sanda sun cafke wani dan takarar gwamnan Borno da suke nema ruwa a jallo a wurin taron Atiku

Da duminsa: ‘Yan sanda sun cafke wani dan takarar gwamnan Borno da suke nema ruwa a jallo a wurin taron Atiku

Grema Terrab, wani dan siyasa kuma mai takarar kujerar gwamna a jihar Borno, ya fada komar ‘yan sanda a yau, Talata, bayan hukumar ta dade da bayyana nemansa ruwa a jallo. Jami’an SARS ne suka kama Terrab a wurin wani taron da Atiku Abubakar ya halarta.

Hukumar ‘yan sanda ta ayyana neman Terrab ruwa a jallo bisa zarginsa da taka rawa a wani laifin kisa da aka yi a wurin wani taron siyasa da aka yi a gidansa tun watan Afrilu.

A yau ne Mista Terrab ya bayyana a garin Maiduguri tun bayan day a bar garin a watan na Afrilu.

Rahotanni sun bayyana cewar Mista Terrab ne da kansa ya sanar da hukumar ‘yan sanda batun kisan, amma duk da haka saida jami’an ‘yan sandan suka kama matar sa tare da tsar eta na tsawon sati biyu. Lamarin day a yi sanadiyar zubewar juna biyu da take dauke da shi.

Da duminsa: ‘Yan sanda sun cafke wani dan takarar gwamnan Borno da suke nema ruwa a jallo a wurin taron Atiku
‘Yan sandan Najeriya

Fastoci da allunan tallar Mista Terrab a matsayin dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar PDP sun shiga kowanne lungu da sako na garin Maiduguri.

Bayan samun rahotannin zuwansa wurin taron, sai jami’an ‘yan sanda sun yiwa wurin kawanya kuma da bayyanarsa keda wuya suka cika hannu da shi.

DUBA WANNAN: Kangararrun matasa sun fasawa kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba kai da jifa

Kokarin Mista Terrab na jan hankalin Atiku domin ya cece shi bai samu cika yayinda jami’an tsaron Atikun suka fita da shi daga wurin taron. An hangi Mista Terrab na rike gefen babbar rigar Atiku domin ya hana a tafi da shi.

Kazalika duk rokon yaransa domin jami’an ‘yan sandan su sake shi bai samu karbuwa ba.

An hana ‘yan jarida daukan hoto ko faifan bidiyon kamun Mista Terrab.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng