Ana kukan targade: An samu bullowar wata sabuwar kungiyar mai suna “Hakika” a arewacin Najeriya
Hukumar sojin Najeriya ta bakin Laftanal TG Iortyom, mukaddashin kwamandan rundunar Ofireshon lafiya dole, mai aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno ta sanar da bullowar wata kungiya mai suna “Hakika”.
Sanarwar ta bayyana cewar kungiyar ta bullo ne a yankin kananan hukumomin Yola ta kudu a jihar Adamawa da Toto a jihar Nasarawa.
Iortyom ya kara da cewar yanzu haka kungiyar karkashin jagorancin Yahaya Ibrahim na daukan dirbobi tare da gindaya masu wasu sharuda da suka hada da daina yin sallah biyar (5) a rana, daina yin azumi da daurewa zina gindi.
DUBA WANNAN: Buhari ya gana da shugabannin kungiyar CAN na jihohin arewa 19, duba hotuna
Hukumar soji ta bukaci ragowar hukumomin tsaro da su saka ido a kan harkokin kungiyar a wuraren da suke aiki da kuma bukatar jama’a su sanar da hukuma harkokin duk wata kungiya ko mutane da basu yarda da shi ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng