Nigerian news All categories All tags
2019: Sanatoci 12, mambobin majalisar wakilai 70 sun dira Kaduna domin nuna goyon baya ga Buhari

2019: Sanatoci 12, mambobin majalisar wakilai 70 sun dira Kaduna domin nuna goyon baya ga Buhari

A kalla sanatoci 12 da mabobin majalisar wakilai 70 ne daga jihohin arewa 7 suka dira jihar Kaduna domin nuna goyon bayansu ga tikitin takarar Buhari da Osinbajo a zaben shekarar 2019 mai zuwa.

Wani daga cikin ‘yan kwamitin day a shirya taron, kuma ya bukaci a boye sunansa, ya shaidawa jaridar Tribune cewar sun shirya taron ne domin jaddada biyayyarsu da goyon baya ga shugaba Buhari a yayin da aka samu bullowar tsagin R-APC a cikin jam’iyyar APC tare da bayyana cewar wani sanata ne jagoran taron.

Mun taru a Kaduna ne domin shiadawa duniya cewar mu halastattun ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ne kuma muna goyon bayan tikitin Buhari da Osinbajo a zaben 2019,” a cewar majiyar Tibune.

2019: Sanatoci 12, mambobin majalisar wakilai 70 sun dira Kaduna domin nuna goyon baya ga Buhari

Sanatoci 12, mambobin majalisar wakilai 70 sun dira Kaduna domin nuna goyon baya ga Buhari

Kazalika, majiyar ta bayyana cewar sun kira ‘yan majalisa daga yankin shugaban kasa ne saboda kowanne dan takara na bukatar goyon bayan yankin day a fito kuma don hakan ne suka shirya taron a yankin arewa maso yamma da shugabari Buhari ya fito.

Ba wai muna cewa babu rigingimu bane a APC amma magoya bayan Buhari ne keda rinjaye a cikin ‘yan majalisu da suka fito daga yankin arewa maso yamma,” majiyar ta fada.

DUBA WANNAN: Ba kanta: Sanatoci 30 da ‘yan majalisar wakilai 60 sun kwatsawa R-APC, zasu tsallaka PDP

Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan majalisa daga jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, da Jigawa da zasu halarci taron, tuni sun isa Kaduna.

Jaridar Tribune ta bayyana cewar ‘yan majalisu 9 sun fito ne daga jihar Kebbi, 7 daga Sokoto, 7 daga Zamfara, 14 daga Katsina, 15 daga Kano, 11 daga Jigawa da kuma 8 daga Kaduna.

A bangaren sanatoci, akwai 2 daga Sokoto, 2 daga Kano, 2 daga Jigawa, 2 daga Kebbi, 2 daga Zamfara da 2 daga Katsina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel