Ba kanta: Sanatoci 30 da ‘yan majalisar wakilai 60 sun kwatsawa R-APC, zasu tsallaka PDP

Ba kanta: Sanatoci 30 da ‘yan majalisar wakilai 60 sun kwatsawa R-APC, zasu tsallaka PDP

Mambobin tsagin R-APC na jam’iyyar APC mai mulki sun kamala shirye-shiryen tsallakawa zuwa jam’iyyar adawa ta PDP nan bada dadewa ba, kamar yadda rahoton jaridar Tribune ya wallafa.

Wata majiya daga cikin tsagin R-APC a majalisar kasa ta shaidawa Tribune din cewar ficewarsu zata kawo canji a kunshin shugabancin majalisun kasar nan. Majiyar ta kara da cewar, ‘yan kwanaki kadan ya rage su fice daga APC.

Majiyar ta bayyana cewar ‘yan majalisar zasu kamala dukkan shiri tare da ficewa daga APC sati daya kafin tafiyarsu hutu ranar 21 ga watan Yuli da muke ciki.

Ba kanta: Sanatoci 30 da ‘yan majalisar wakilai 60 sun kwatsawa R-APC, zasu tsallaka PDP
Sanatoci 30 da ‘yan majalisar wakilai 60 sun kwatsawa R-APC, zasu tsallaka PDP

Shugabannin majalisun kasa, Bukola Saraki da Yakubu Dogara, ne ke jagorantar ‘yan majalisun da zasu canja shekar domin ganin cewar sun samu rinjayen da zai basu dammar cigaba da rike mukamansu.

‘Yan majalisar na son kafa hujja da rikicin da ya dabaibaye APC a matsayin dalilinsu na ficewa daga jam’iyyar, kamar yadda yake a sashe na 68(1,g) na kundin tsarin mulkin kasa day a bayyana cewar, dan majalisa zai iya canja sheka ne kawai idan da akwai rabuwar kai ko rikic cikin jam’iyyar day a ci zabe.

DUBA WANNAN: Gwamnan APC zai fice daga jam’iyyar saboda fin karfi da tsohon gwamna kuma sanata mai ci ke nuna masa

Mambobin majalisar sun fito ne jihohin arewa da suka hada da, Kano, Adanawa, Sokoto, Oyo, Kwara, Kogi, Kaduna, Bauchi, Benuwe da sauran su.

Tsagin R-APCya kunshi mambobin jam’iyyar PDP da suka shiga APC kafin zaben 2015 da kuma wasu ‘yan APC da basa jin dadin yadda tafiyar gwamnatin jam’iyyar tasu ke tafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel