Buhariyya: Wani ya babbaka kansa saboda bakin cikin rayuwa a Legas, yana can rai kwa-kwai

Buhariyya: Wani ya babbaka kansa saboda bakin cikin rayuwa a Legas, yana can rai kwa-kwai

- Anyi yunkurin kashe mishi wutar amma mutumin ya dinga gudu yana cin wutar, wanda yayi sanadiyyar gudun mutane domin tsoron kada wutar ta kama su

- A lokacin da aka kashe wutar, ya riga ya fadi bai san halin da yake ciki ba

- Yan sanda daga Ogudu suka kwashe shi sai asibiti

Buhariyya: Wani ya babbaka kansa saboda bakin cikin rayuwa a Legas, yana can rai kwa-kwai
Buhariyya: Wani ya babbaka kansa saboda bakin cikin rayuwa a Legas, yana can rai kwa-kwai

Wani mutum da ba a san ko waye ba har yanzu, ya sa wa kanshi wuta a ranar laraba, a kofa shiga Omole Estate, Phase 1,jihar Legas.

A jiya ne likitoci a sashin taimakon gaggawa na asibitin jihar Legas sukayi ta kokarin ceto ran mutumin, wanda a lokacin bai ma san inda kan shi yake ba.

Ganau ba jiyau ba sunce mutumin zai kai kimanin shekara 28 a duniya, ya bullo gurin karfe 3 na rana, duk wani yunkurin hana shi kaiwa karshen bargon ya tashi a banza. Inda ya watsa ma kanshi wani abu da ake zargin fetur ne, sannan ya kyasta ashana.

Anyi yunkurin kashe mishi wutar amma mutumin ya dinga gudu yana cin wutar, wanda yayi sanadiyyar gudun mutane domin tsoron kada wutar ta kama su.

A lokacin da aka kashe wutar, ya riga ya fadi bai san halin da yake ciki ba.

Yan sanda daga Ogudu suka kwashe shi sai asibiti.

DUBA WANNAN: OPC zata fara aikatawa Makiyaya a Kudu

Majiyar mu ta sanar damu cewa babu wanda yaje ofishin yan sandan ko asibitin a matsayin Dan uwan mutumin.

Jami'in huldar da jama'a na yan sandan jihar Legas, Chief Superintendent Chike Oti, ya tabbatar da cewa mutumin yaso kashe kan shi ne.

Kwamishinan yan sandan jihar Legas ya bada umarnin a gaggauta kai mutumin asibiti kuma bayan warkewar shi za a fara bincike akan yunkurin kisan kan shi da yayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel