Nigerian news All categories All tags
Siyasar Kaduna: An yi wani zaman sirri tsakanin babban Sanatan APC da manyan ‘Yan PDP

Siyasar Kaduna: An yi wani zaman sirri tsakanin babban Sanatan APC da manyan ‘Yan PDP

An yi wani zama a boye jiya tsakanin Sanatan Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna ta Arewa watau Suleiman Othman Hunkuyi da ‘Yan Majalisar da ke Jam’iyyar adawa na PDP a Jihar. kamar yadda mu ka ji.

Siyasar Kaduna: An yi wani zaman sirri tsakanin babban Sanatan APC da manyan ‘Yan PDP

Sanatan APC Suleiman Hunkuyi ya gana da wasu 'Yan PDP a Majalisa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanatan APC na Kaduna Suleiman Hunkuyi ya zauna da wasu manyan Jam’iyyar PDP da kuma wasu ‘Yan Majalisar Wakilan Jihar da ke karkashin Jam’iyyar adawa na PDP a Majalisar Dattawa.

Sanata Suleiman Hunkuyi ya gana ne da wasu ‘Yan Majalisar adawa na Jihar. Daga cikin wadanda su ka halarci wannan taro da aka yi akwai ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Yankin Soba Hon. Musa Soba da kuma Rabiu Lawal na Lere.

KU KARANTA:

An yi wannan taro ne a cikin Majalisar Dattawa domin ganin yadda za a fara shirin doke Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Kaduna a zabe mai zuwa. ‘Yan Majalisar na rikici ne da Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai wanda abin yayi kamari.

Shi dai Sanatan ya bayyana cewa ‘Yan Jam'iyyar PDP sun kawo masa ziyara ne domin jawo su cikin Jam’iyyar su. Sanata Hunkuyi yace kuma ba a kin ta mutane don haka za su duba halin da ake ciki domin kuwa ba ayi da su a Jam’iyyar APC.

Jiya kun ji cewa Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa shakka babu wasu za su tattara su tsere daga Jam’iyyar APC kwanan nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel