Shugaba Buhari mutum ne Nagari - Sarkin Katsina

Shugaba Buhari mutum ne Nagari - Sarkin Katsina

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya bayyana cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai nagarta kuma ko tantama ba bu zai samu goyon bayan al'ummar jihar Katsina domin cikar kudirin sa na neman kujerar sa a karo na biyu.

Sarkin ya bayar ta tabbacin sa ga shugaba Buhari da cewar zai samu goyon bayan al'ummar jihar Katsina 100 bisa 100 a zaben 2019.

Sarkin ya bayyana hakan yayin da shugaban kasar ya kai ziyarar jajantawa al'ummar jihar dangane da ibtila'in ruwan sama da ya afku a kwanakin baya kadan da ya salwantar da rayukan mutane 11 da kuma dukiya ta kimanin naira biliyan 2.3 cikin jihar.

Uba ga talakawan ya bayyana cewa shugaba Buhari ya kafa tsarkakken tarihi yayin da ya rike mukaman gwamna da shugaban kasa na lokacin mulki soji da kuma shugaban asusun kudaden man fetur.

Shugaba Buhari yayin barin jihar Katsina zuwa kasar Mauritania
Shugaba Buhari yayin barin jihar Katsina zuwa kasar Mauritania

Ya kara da cewa, Shugaba Buhari jagora nagari da babu abinda ya sanya a gaba face damuwa gami da kulawa da talakawan sa, wanda wannan shine babban dalili da ya kasance abin soyuwa a zukatan su.

Shugaban kasar wanda ya ziyarci jihar ta Katsina domin jajantawa al'ummar da ibtila'in ruwan sama ya afkawa. Ya kuma sha alwashin cewa gwamnatin tarayya za ta tallafa ma su daidai gwargwado.

DUBA WANNAN: EFCC ta gurfanar da wani Tsohon Minista da wasu Mutane 4 bisa laifin Almundahana

Shugaba Buhari ya ciga da cewa, gwamnatin tarayya za ta turo wakilanta domin aiwatar da kididdiga da tantance adadin asara da wannan ibtila'in ya janyo cikin jihar.

A nasa jawaban, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa ibtila'in da ya afku ya janyo asarar dukiya ta kimanin naira biliyan 2.3, inda ya ce asarar da ya janyo a makarantu kadai ta kai ta kimanin Naira miliyan dari biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng