Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da aikin hanya daga Kano zuwa Abuja
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana mun samu rahoton cewa, a ranar yau ta Talata ne gwamnatin tarayya ta fara kaddamar da katafaren aiki gadan-gadan na sake gina babbar hanyar titin mota daga jihar Kano zuwa Abuja.
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin tarayya yayin zaman majalisar zantarwa ta bayar da lamunin gudanar da wannan katafaren aiki da ta danka kwangilar sa ta kimanin N155, 470,626,078.07 a hannun kamfanin Julius Berger Nigeria Plc tun watan Dasumba na shekarar 2017 da ta gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa, kamfanin tare da gwamnatin tarayya sun yi yarjejeniyar kammala wannan muhimmin aiki cikin watanni 36 masu gabatowa.
Ministan makamashi, ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, shine zai kaddamar da wannan aiki yayin da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da takwaran sa na jihar Kaduna, Nasir El Rufai, Ministan Birnin tarayya, Muhammad Bello za su halarci wannan biki na kaddamar da katafaren aiki.
DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP tayi kaca-kaca da Fadar Shugaban Kasa kan Kashen-Kashen Jihar Filato
Sauran wadanda za su halarci bikin sun hadar da; kananan Ministoci biyu; Mustapha Baba Shehuri da Suleiman Hassan Zarma da kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan aikace-aikace; Sanata Kabiru Gaya.
A na sa ran wannan muhimmin aikin hanya zai zamtomahaɗa tsakanin Kudu da Arewacin Kasar nan domin saukaka cunkoso da jerin gwanon Motoci da yake ta faman karuwa kan babbar hanyar tun gabanin shekarar 1990.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng