APC ba addini bane don haka zan fita na bar ta da miyagu – Sanata Shehu Sani

APC ba addini bane don haka zan fita na bar ta da miyagu – Sanata Shehu Sani

Wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana jam’iyyar APC a matsayi hadakar miyagun mutane marasa gaskiya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Shehu ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi a shirin kowani gauta na gidan rediyon Freedom, inda ya nuna bacin ransa da yadda ake tafiyar da jam’iyyar APC, wanda yace hakan akasin yadda aka gina tubalin jam’iyyar ne a tun farko.

KU KARANTA: BTsautsayi baya wuce ranarsa: Wani katafaren gini ya ruguzo akan wasu Leburori 4

“An shirya za ayi adalci a jam’iyyar APC a baya, amma a yanzu an koma rashin gaskiya, abu biyu ne dama mutum ba zai iya rabuwa dasu ba, iyayenka ba zaka iya canzasu ba, haka ma addininka, don haka tunda dai jam’iyyar ba addini bace, zan fita daga cikinta. zamu sanar da inda zamu koma” Inji shi.

APC ba addini bane don haka zan fita na bar ta da miyagu – Sanata Shehu Sani
Sanata Shehu Sani

Sanatan ya bayyana jam’iyyar APC a jihar Kaduna a matsayin mayaudariya, wanda ta gagara cika alkawurran da ta daukan ma al’ummar jihar: “Sun yi alkawarin daukan ma’aikata dubu goma sun buge da korar dubu hamsin, sun kasa yi ma jama’a ayyuka, sun yi alkawarin ingantaccen zabe sun buge da satar akwati.”

Dangantaka dai ta yi tsami ne a tsakanin Shehu Sani da gwamnan jihar Kaduna tun bayan kammala zabukan shekarar 2015, inda Sanatan ke zargin gwamnan ya mayar da shi saniyar ware, shi kuma gwamnan ke zargin Sanatan na sunsunan kujerarsa don haka yake yi masa zagon kasa.

Wannan rikici nasu ya kara ruruwa bayan da Sanatan yayi kutunkutun a matsayinsa na shugaban kwamitin ciyo bashi na majalisar dattawan Najeriya, ya hana gwamnatin jihar samun bashin dala miliyan 300 da babban bankin Duniya ta shirya bata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel