Dakarun sojin sun kara yiwa mayakan kungiyar Boko Haram 23 raga-raga, duba hotunan makaman da aka samu
A jiya, Talata, 11 ga watan Yuni, dakarun sojin Najeriya tare da hadin gwuiwar sojojin jamhuriyar Kamaru suka yiwa wasu mayakan kungiyar Boko Haram kaca-kaca tare da kwato wasu makaman da kayan da mayakan ke amfani da su.
Daga cikin makaman da dakarun sojin suka yi nasarar kwatowa daga hannun mayakan akwai bindigu kirar AK 47 guda 6, wasu Karin bindigu 2 samfurin FN, alburusai masu yawa da kwanson su da kuma Babura guda 2.
Sojin sun yi nasarar kasha mayakan kungiyar ta Boko Haram guda 23 tare da raunata wasu da dama.
Kafin wannan arangama, dakarun sojin sun yi nasarar kakkabe ragowar mayakan kungiyar Boko Haram daga maboyar su a kauyukan dake makwabtaka da tekun Chadi da suka hada da; Bulakeisa, Tumbuma Babba, Abbaganaram, Dan Baure da sauran su.
DUBA WANNAN: Ki taimake ni, ke ma fa kirista ce - Karanta yadda gwamna Dariye ya yi ruwan magiya ga alkaliya bayan yanke masa hukunci
Hukumar soji, tab akin darektan yada labarai, Texas Chukwu, ta shawarci jama’ar jihar Borno da suke gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani motsin mutane da basu yarda das hi domin daukan mataki a kan lokaci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng