'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

Hukumar Yan sanda reshen Jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar mutane takwas a wata rikici da ya barke tsakanin yan baranda da yan banga a jiya Litinin a karamar hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato.

Jami'ar hulda da jama'a na rundunar, Cordelia Nwawe ta shaidawa yan jaridar cewa ana kyautata zaton mutane takwas ne suka rasu ciki har da wani dattijo da yan barandan su kayi kokarin sacewa.

Ms Nwawe ta kara da cewa har yanzu ana cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin, ta kuma ce ana kyautata zaton yan barandan sun zo ne daga kauyukan jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sakkwato.

'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato
'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 8 a arangamar da 'yan baranda su kayi da 'yan banga a Sakkwato

KU KARANTA: An kuma: 'Yan fashi sun yi mumunar ta'asa a hanyar Kaduna-Abuja

Ta kuma ce kwamishinan Yan sanda na jihar ya zuyarce kauyen da abin ya faru don yin jaje ga iyalen wadanda abin ya shafa tare da tabbatar musu cewa yan sanda za su binciko wadanda suka aikata wannan laifin.

Sai dai a wata rahoton, an ce mutane 13 ne suka rasu sakamakon yunkurin da yan barandan su kayi na sace wani dattijo ranar Asabar a kauyen Dan Tasango a Gundumar Gebe.

A cewar wani ganau, yan barandan sun harbe dattijon ne saboda ya ki yarda su tafi dashi, hakan ne yasa yan bangan garin suka hada kai don bin sahun yan barandan.

Majiyar ya cigaba da cewa 'yan barandan sunyi wa yan bangan kwantar bauna a hanyar Kamarawa-Barafawa inda akayi musayar wuta inda yan barandan suka kashe yan banga bakwai su kuma aka kashe musu mutane biyar.

Sai dai yan barandan sun kwace gawawakin mutane biyar din da aka kashe musu kamar yadda suka saba saboda kar a gane ko su wanene.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel