Wani saurayi ya kama budurwar sa da wani gardi kwanaki 13 saura daurin aure
Wata budurwa dake shirin amarcewa ta ga ci ta ga rashi bayan saurayin da zata aura ya kama ta tana lalata da wani gardi.
Wata kawa ce ga amaryar, @quinsmilez, ya kwarmata labarin a shafin sa na tuwita tare da bayyana cewar laifin na saurayin ne da ya aike ta karbar sako wurin abokin sa da ya fi shi kudi da kyau.
Kawar amaryar mai sunan gaskiya Queen Idoko ta bayyana matukar kaduwa da dimuwa ga abinda ya faru ga kawar ta tare yin tambayar me yasa wasu ke cin amanar soyayya.
Queen t ace idan an bi ta barawo ya kamata a bi ta mabi sahu, saboda tun farko saurayin ne ya jawo faruwar hakan ta hanyar aika budurwar sa zuwa ga mutumin day a yaudare ta hart a kai ta aikata wannan laifi.
DUBA WANNAN: Tsohon babban dan sanda ya bayyana dalilin firgitar Obasanjo da gwamnatin Buhari
A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, wani matashi, Anthony Murimi, ya jawo barkewar hargowa bayan yah aye kan kololuwar karfen sabis tsirara tare da tube kayan sa domin gujewa kamun ‘yan sanda.
A yau, Litinin, ne hukumar ‘yan sanda ta gurfanar da matashin mai shekaru 23 a gaban wata kotu dake Embu a kasar Kenya bisa tuhumar sa da yunkurin kasha kan sad a kuma yin kutse cikin muhallin dab a shi da hurumin shiga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng