Kashedi: Sule Lamido yace sama zata fado a duk ranar da Buhari ya kama Jonathan
Tsohon gwamnan jihar Jigawa dake fuskantar tuhume tuhumen kan zargin cin satar kudaden al’umma, Alhaji Sule Lamido ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewa shima yaci kudin makamai, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Lamido ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani, Facebook, inda yace tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan akan al’amuran tsaro, Sambo Dasuki ya baiwa Buhari motoci masu sulke guda biyu bayan da Boko Haram ta kai masa hari a Kaduna.
KU KARANTA: Zakaran da Allah ya nufa da Cara: Cikakken jerin sunayen shuwagabannin APC na jihohi 36
Bugu da kari Lamido yace me yasa Buhari ya gagara kama Jonathan, bayan duk wadanda ake tuhuma suna na da nasaba da tsohon shugaban?
“Wai a ina Dasuki ya samu dala biliyan 2.5 da ya rarraba ma manyan mutane yayin da ake gab da zaben 2015, laifin da yasa har yanzu yake daure a hannun hukumar DSS? A ina Nanadi ta samu makudan biliyoyi da ta rarraba ma jihohi wanda yasa a yanzu haka take gaban Kotu?
“Ga amsa, dukkaninsu sun samu kudaden ne daga babban bankin Najeriya dake karkashin shugaban bankin na yanzu, Godwin Emefeile, kuma tsohon shuhgaba Jonathan ne ya bada wannan umarni.” Inji shi.
Daga karshe Lamido dake takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP yace: “Don haka tunda Alkali Binta Nyako ta yanke hukucin cewar bai kamata a kama duk wanda aka basu umarnin yin laifi da laif ba, Gwmanatin Buhati ba zata iya kama Jonathan bane, ta gwana mu gani, da sai sama ta fado.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng