Gasar kofin Duniya: Shugaban Majalisar Dattawa ya ba ‘Yan kwallon Najeriya gudumuwa

Gasar kofin Duniya: Shugaban Majalisar Dattawa ya ba ‘Yan kwallon Najeriya gudumuwa

- Shugaban Majalisar Dattawa ya jinjinawa ‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya

- Bukola Saraki ya yabawa Kyaftin din kungiyar da kuma mai kula da ‘Yan wasan

- Saraki ya ba ‘Yan kwallon Najeriya da ke shirin barin gida gudumuwar Miliyoyi

Mun samu labari a Ranar Laraban nan cewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya watau Bukola Saraki ya kai ziyara har dakin da ‘Yan wasan Super Eagles su ke kwana a Abuja domin yi masu sallama.

Gasar kofin Duniya: Shugaban Majalisar Dattawa ya ba ‘Yan kwallon Najeriya gudumuwa
Super Eagles za ta je Rasha domin buga Gasar kofin Duniya

Abubakar Bukola Saraki ya kai wa ‘Yan kwallon na Najeriya da ke shirin tafiya zuwa Kasar Rasha domin cin Gasar kofin Duniya na bana ziyarar da ba su yi tsammani ba. Bukola Saraki ya yabawa ‘Yan wasan Kasar da irin kokarin da su ke yi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gana da 'Yan wasan Najeriya

Sanata Bukola Saraki ya kuma jinjinawa kokarin Kyaftin din Najeriya John Mikel Obi na jagorantar Kungiyar ta Super Eagles salin-alin. Saraki yace Mikel Obi da ‘Yan wasan na sa ba su kokawa da irin karancin sakayyar da ake yi masu.

Shugaban Majalisar Dattawan yace yana bibiyar Super Eagles kuma ta tabbata cewa yanzu Kungiyar a dunkule ta ke. Saraki yace ‘Yan Najeriya za su marawa ‘Yan wasan baya a Gasar inda ya ba su gudumuwar kudi har Naira Miliyan 18.

Haka kuma dai Sanatan Kasar ya yabawa kokarin Gernot Rohr wanda shi ne babban Jami’in da ke kula da Super Eagles. A makon nan dai Najeriya ta yi kunnen doki da ta kara da Kasar Congo a Garin Ribas.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng